ABNA24 : A cikin wata sanarwa da Birtaniya ta tsara da sunan kwamitin mai mambobi 15, ta yi kira da a fadada shirin sulhu a tsakanin al’ummar kasar ta Libya.
Har ila yau, kwamitin tsaron na MDD ya yi kira da a ci gaba da aiki da tsagaita wutar yakin da ta fara aiki tun cikin watan Oktoba, haka nan kuma janye dukkanin sojojin kasashen waje da suke cikin kasar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai bangarori daban-daban na kasar Libya su ka cimma yarjejeniya da kuma zabar sabuwar gwamnati a wani taro da su ka yi a birnin Geneva na kasar Switzerland, a karkashin sa ido da kulawar MDD.
Kasar Libya ta fada cikin rikicin siyasa da na tsaro tun bayan kifar da gwamnatin Mu’ammar Khaddafi da kungiyar yarjejeniyar tsaro ta NATO ta yi a 2011.
342/